An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

- Shugaba Buhari dai ya watsa wasu hotunan sa kuda 3 a yayin da yake rangadi a gonar sa

- Shugaba Buhari yayi anfani da wannan damar wajen cusawa 'yan Najeriya ra'ayin noma

- Sai dai 'yan Najeriya da dama sun yiwa lamarin mummunar fahimta

A jiya ne dai rudani da fada suka kacame a dandalin zumunta na Tuwita bayan da shugaba Buhari a bayyana a cikin wasu kyawawan hotuna a gonar sa dake Daura.

A tare da hotunan dai shugaban na Najeriya ya kuma bayyana cewa yana so yayi anfani da wannan damar ne wajen ganin ya cusawa yan kasar dabi'ar noma da kiwo domin samun dogaro da kai.

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya
An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

KU KARANTA: Tsohon ministan ilimin Najeriya ya rasu

Legit.ng dai ta samu cewa a wani bangare kuma na mutanen sai suka yi wa lamarin mummunar fahimta inda suka zargi shugaban da ba dabbobin nasa kulawar da tafi 'yan Najeriya bayan da aka ga shanun sun yi bul-bul fiye da yadda suke a shekarar 2015.

Haka nan wani bangare na 'yan Najeriyar haka zalika sun bayyana cewa shanun a yanzu sun fi 150 kamar yadda suke a shekara ta 2015 jim kadan bayan hawa kan karagar mulkin sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng