Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi

Burin tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na zama shugaban kasar Najeriya a shekara 2019 ya fara zama kamar bula, wanda bata kumfa, musamman biyo bayan babban taron jam’iyyar PDP.

Sakamakon zaben daya gudana a ranar Asabar 9 ga watan Disamba ya fitar da sabbin shuwagabannin jam’iyyar, wanda hakan ke nufin gwamnonin jam’iyyar, tare da tsofaffin gwamnonin jam’iyyar ne ke da rike da jam’iyyar a tafin hannunsu.

KU KARANTA: Duniya juyi juyi, tsohon Kaakakin jam’iyyar PDP ya fuskanci wulaƙanci a hannun jam’ian tsaro

The Nation ta ruwaito wasu daga cikin jiga jigan jam’iyar da ka iya lalata burin Atiku sun hada da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, na Ekiti, Fayose, da na Gombe, Dankwambo, Sanata David Mark, Ike Ekweremadu, Akpabio, Shema, Tanimu Turaki, Babangida ALiyu, Sule Lamido, Aminu Wali da Zainab Maina.

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi
Atiku

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani jigo a jam’iyyar yana fadin “Akwai kalubale da dama dake gaba Atiku, musamman gwamnoni, da kuma yan takarkarun shugaban kasa dake jam’iyyar, haka zalika wasu gwamnonin jam’iyyar na goyob bayan Makarfi ya tsaya takara, sakamakon yadda ya tafiyar da jam’iyyar PDP a lokacin da take cikin rikici.

“Haka zalika akwai rade rade a jam’iyyar na cewa zata gayyato Tambuwal don ya tsaya mata takara, don haka ya zama wajibi Atiku ya san na yi tun yanzu.” Inji majiyar.

Sauran jiga jigan iyayen jam’aiyyar da zasu koma gefe a yanzu sun hada da Tsohon shugaban kasa Badamai Babangida, Goodluck Jonathan, Namadi Sambo, Mukhtar Ramalam Yaro, Ibrahim Mantu, Nenadi Usman da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng