Nigerian news All categories All tags
Duniya juyi juyi, tsohon Kaakakin jam’iyyar PDP ya fuskanci wulaƙanci a hannun jam’ian tsaro

Duniya juyi juyi, tsohon Kaakakin jam’iyyar PDP ya fuskanci wulaƙanci a hannun jam’ian tsaro

Duniya mai ido a tsakar ka, Duniya juyi juyi, hakazalika duk wanda ya auri Duniya, toh lallai Duniya zata sake shi saki uku zuwa wani lokaci kalilan, kamar yadda bahaushe ke fadi.

A yayin babban taron jam’iyyar PDP daya gudana a ranar Asabar 9 ga watan Disamba ne jami’an tsaron dake kula da taron suka cumimiye tsohon Kaakakin jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, bayan sun ja hankalinsa ya ki ji.

KU KARANTA: Abin kunya: Jami’in hukumar kare hadɗura ya gwada ƙwanji da wata mata a kan titi

Sahara Reporters ta ruwaito tirka tirkan ta samo asali ne a lokacin da Metuh ya isa inda ake gudanar da babban taron,d a isar sa sai ya nemi shiga rumfar manyan yan jam’iyya, amma sai jami’an tsaro suka dakatar da shi, suka ce masa ba shi da wuri a shingen, musamman ta yadda an riga an rubbuta sunayen manyan baki a kowanne kujera.

Duniya juyi juyi, tsohon Kaakakin jam’iyyar PDP ya fuskanci wulaƙanci a hannun jam’ian tsaro

Yayin takaddamar

Abinka da wanda Duniya ta yi ma sake uku, nan fa ya fara ihu yana hauma hauma, wai shi a dolen doliya sai ya shiga rumfar, tunda a tunaninsa, irin kokarin da yayi ma jam’iyyar a baya, musamman a gabanin zabukan 2015, bai dace a hana shi shiga rumfar ba.

Ga bidiyon yadda lamarin ya faru:

Ana cikin haka ne sai shugaban shirya taron, kuma gwamnan jihar Delta, Patrick Okowa ya shiga tsakani, inda ya tabbatar ma Metuh cewa ba zai bari ya shiga shingen ba, sa’annan ya sa aka raka shi zuwa shingen mutanen jihar Anambra, yan garinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel