Abuja: Gwamnatin Buhari tana kan hanyar da ta dace – Inji shugaban Peace Corps

Abuja: Gwamnatin Buhari tana kan hanyar da ta dace – Inji shugaban Peace Corps

- Shugaban Peace Corps ya ce gwamnatin Buhari na kan hanyar da ta dace

- Shugaban ya ce, yana matukar damuwa game da sukar da ake yi wa wannan gwamnatin

- Akoh ya bayyana cewa hukumar ta yi imani cewa shugaba Buhari na yin abin da ya dace a yaki da cin hanci da rashawa

Shugaban Peace Corps ta kasa, Mista Dickson Akoh, ya bayyana cewa hukumar tana da tabbacin cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na kan hanyar da ta dace.

Shugaban ya kuma nuna damuwa game da sukar da ake yi wa gwamnatin.

Da yake jawabi a wani bikin ƙarshen shekara na hukumar a Abuja, Akoh ya bukaci 'yan Najeriya su ba shugaba Buhari damar wa’adi na biyu a ofis don kammala manyan ayyukan ci gaban da ya fara.

Abuja: Gwamnatin Buhari tana kan hanyar da ta dace – Inji shugaban Peace Corps
Shugaban Peace Corps ta kasa, Mista Dickson Akoh

Ya ce: "Muna da imani cewa gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari na yin abin da ya dace a yaki da cin hanci da rashawa da ta’addanci da kuma bunkasa tattalin arzikin".

KU KARANTA: Za mu gyara hanyar Kaduna zuwa Kano don kullum sai mota ta fadi - Buhari

Legit.ng ta tattaro cewa, Akoh ya bukaci gwamnati da masu fada a ji a kasar cewa suyi kokarin samar da kayan aiki na asali a yankunan karkara don rage matsalolin ƙaura daga ƙauyuka zuwa birane.

Akoh ya yi alkawarin cewa, hukumar za ta hada kai tare da dukan jami'an tsaro don ci gaban kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng