Libya : Yadda na kwana da larabawa 18 a cikin dare daya – Yar jihar Edo mai shekaru 19

Libya : Yadda na kwana da larabawa 18 a cikin dare daya – Yar jihar Edo mai shekaru 19

- Wata yar Najeriya ta bayyana irin wahalar da ita da kawartaa suka sha kasar Libya

- Yarinyar mai shekaru 19 ta ce bata taba ganin mugayen mutane a duniya kamar Larabawa ba

- A dare daya Larabawa 18 suka yi zina dani inji yarinyar

Wata yar Najeriya wace ta kasance daya daga cikin yan matan da aka dawo da su daga kasar Libya, ta bayyana yadda larabawa 18 suka sadu da ita a cikin dare daya.

Daruruwan yan Najeriya da aka yi fataucin su a kasar Libya wanda mafi akasarin su haifaffun jihar Edo ne, sun fara dawowa.

Yarinya mai shekaru 18 daga jihar Edo wanda bata son a bayyana sunanta, ta fadawa yan jarida irin wahalar da ta sha a kasar Libya.

Yarinyar ta fadawa majiyan jaridar Telegraph cewa kawarta ta roke ta, suka yi wannan tafiya.

Sun bar Najeriya ne a watan Mayu na shekara 2017 tare da wata mata dake daukar nauyin mutane zuwa kasar waje.

Libya : Yadda na kwana da larabawa 18 a cikin dare daya – Yar jihar Edo mai shekaru 18
Libya : Yadda na kwana da larabawa 18 a cikin dare daya – Yar jihar Edo mai shekaru 18

Yarinyar ta ce Matar ta fada musu cewa cewa za ta samar su aiki kasar Jamus, sai kuma rayuwar su ta kasance a kasar Libya.

KU KARANTA : An yanke wa Dogara hukuncin shekaru 10 a gidan kaso baya an kama shi da laifin zamba

“Bana son na rika tuna irin kuncin rayuwan da na fuskanta a kasar Libya, Ina matukar farinciki da Allah ya sa na dawo Najeriya.

“Ina koyan kasuwanci ne a Najeriya kafin kawata ta rinjaye ni nayi wannan tafiya, ko iyaye na ba su san nayi tafiya ba.

Muna isa kasar Libya matar da ta dauki nauyin tafiyar mu, ta mika mu zuwa ga hannun wasu mugayen Larabawa ta ce mana mun kusan shiga kasar Italiya.

Mafi munin abun da ya faru dani shine ranar da Larabawa 18 suka sadu dani a cikin dare daya, wannan abun ne da bazan taba iya manatawa dashi a rayuwata ba.

“Ban taba ganin mungayen mutane a duniya kamar Larabawa, bayan sun gama amfani dani sai suka bani naira N15,000, bayan haka wanda suka dauki nauyi na suka anshi naira 10,000 suka barni da N5,000.

“Kawata da muka yi wannan tafiya tare ta mutu, na gode wa Allah da ya ceci rayuwa na. Ban taba tunanin zan kara ganin watan Disamba ba.

“Har yanzu akwai darurruwan mutane a kasar Libya dake bukatar ceto," Inji yarinyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel