Yanzu-Yanzu: Makami mai linzami daga Falasdina ya dira a kudancin yankin Israila

Yanzu-Yanzu: Makami mai linzami daga Falasdina ya dira a kudancin yankin Israila

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni da cewa a yayin wani labari da dumin sa, makami mai linzami da ake kyautata zaton daga yankin Falasdinawa yake ya dira a yankin kudancin Isra'ila a wani gari da ake kira Sderot da daren juma'ar nan da ta gabata.

Sojojin yankin Isra'ila din ne dai suka sanar da hakan yayin da abun ya faru sai dai kawo yanzu babu bayanan alkaluman adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata sakamakon harin.

Yanzu-Yanzu: Makami mai linzami daga Falasdina ya dira a kudancin yankin Israila
Yanzu-Yanzu: Makami mai linzami daga Falasdina ya dira a kudancin yankin Israila

KU KARANTA: Akwai yiwuwar kai hari a manyan garuruwan Arewa

Legit.ng dai ta samu cewa wannan ne karo na uku da makamin mai linzami ya sauka a cikin Isra'ila daga Falasdinu tun bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ayyana Jerusalem a matsayin sabuwar Hedikwatar kasar Isra'ila.

Shuagbannin kasar ta Amurka na baya dai duk sun kaucewa wannan bukata ta Isra'ilawa don gudun barkewar fitina. Haka ma kasashen larabawa sun nuna damuwa ga wannan matsayi na Trump da su ke ganin ba zai haifar da alheri ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng