Madalla! Darajar Naira ta kara yin sama a kasuwar 'yan canji
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa kudin Najeriya na Nera sun kara samun daraja a kasuwannan duniya na shige da fice watau Investor and Exporter (I&E) a turance inda yanzu haka ake sayar da dalar Amurka a kan Naira 360.
Alkaluma dai daga kasuwannin duniyar sun nuna cewa Naira din dai ta kara daraja da kwabo 62 a kasuwar a tsakanin ranar Laraba da kuma Alhamis lamarin da yayi sanadiyyar sake ruguzowar takardar dala.
KU KARANTA: An karrama kungiyar Izala a kasar Sifen
Legit.ng haka zalika ta samu cewa a kasuwannin 'yan canji na bayan fage kuwa farashin dalar yana nan a Naira 363 ne a tun bayan kwanaki hudu da suka gabata inda aka samu daidaiton.
Haka ma dai mun samu cewa Babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria, CBN ya bayyana cewa yanzu haka dai baitul malin kasar nan ta cika ta tumbatsa inda take kimanin dala biliyan 38.2, matsayin da bata taba kaiwa ba a cikin shekaru 3 na mulkin shugaba Buhari.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng