Ta kara tsawo: An zargi uwa da yayan Maryam Sanda da hannu dumu-dumu cikin kisan Bilyaminu
A wani yanayi mai dauke da sabon salo, jami'an 'Yan sandan Najeriya masu gabatar da kara a gaban kotu a jiya sun zargi uwa da kuma yayan Maryam Sanda da hannu dumu-dumu a cikin laifin kisan mijin ta Bilyaminu da ya faru a satin baya a garin Abuja.
Wannan dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu na kunshe ne a cikin wani daftarin kundin laifuka da jami'an 'yan sandan suka gabatar a yayin zaman kotun da aka yi jiya a garin na Abuja.
KU KARANTA: Atiku ya sake kada Buhari a zaben gwaji
Legit.ng dai ta samu cewa a kwanan baya 'yan sanda suka cafke Maryam Sanda din bayan da tayi sanadiyyar mutuwar mutuwar mijin ta mai suna Bilyaminu Bello dake zaman da ga tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP.
Sai dai yanzu a sabon daftarin kundin zargin, 'yan sanda sun bayyana cewa suna zargin uwar Maryam din din da kuma yayan ta mai suna Aliyu da ma wata macen daban mai suna Sadiya Aminu da laifin kokarin badda shaidun kisan ta hanyar goge jinin kisan.
Haka ma dai mai karatu dai iya tuna cewa hukumar nan da ke binciken almundahana ta kudade ta gwamnatin tarayya watau Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) a baya tana binciken mahaifiyar Maryam din bisa laifin handame kudaden jama'a.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng