Matashin da ya yi ma wani Yaro yankan rago, ya gamu da hukuncin kisa ta hanyar rataya

Matashin da ya yi ma wani Yaro yankan rago, ya gamu da hukuncin kisa ta hanyar rataya

Wata babbar Kotun jihar Nassarawa ta yanke ma wani matashi hukuncin kisa bayan ta kama shi da laifin kisan wani karamin yaro Samuel Danjuma tun a shekarar 2012 a jihar Nassarawa.

Muryam Amurka, VOA, ne ta ruwaito labarin, inda ta ce alkalin kotun, mai sharia James Abundaga ya tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan Yakubu John, wanda aka tabbatar da shi ne ya yi ma Samuel Danjuma, mai shekaru 7 kisan gilla, ta hanyar yi masa yankan rago.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Kotu ta miƙa ma gwamnati naira miliyan 329 da wani babban jami’in gwamnati ya karkatar

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar 22 ga watan Yulin shekarar 2012 ne Yansanda suka cafke John tare da Ishaya Daklung, inda aka kama John dauke da kan yaron bayan ya yanke kansa a bakin rafi Angwan Galadima dake karamar hukumar Nassarawa.

Alkali ya ce hukuncin kisan da ya yanke ma John yayi daidai da sashi na 221 na kudin hukunta manyan laifuka na jihar Nassarawa, bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa, haka zalika ya yanke ma Daklung hukuncin zaman Kurkuku na tsawon shekaru 4, tare da horo mai tsanani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng