Saki ko cigaba da dauri: Kotun Allah-ya-isa zata yanke hukunci kan Dasuki 2 ga watan Maris
Babbar kotun kolin tarayyar Najeriya da akan yi wa lakani da kotun Allah-ya-isa ta sanar da 2 ga watan Maris a matsayin ranar da zata yanke hukuncin da tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Jonathan shawara game da harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki mai ritaya bisa ga cigaba da tsare shin da ake yi ba a bisa ka'ida ba.
Gungun alkalai na mutum biyar ne dai karkashin jagorancin babban alkali Dattijo Mohammed ne suka sanar da ranar ga dukkan bangarorin da shari'ar ta shafa bayan da suka kammala saka ranar.
KU KARANTA: Karin kudin mai: Gwamnatin tarayya tayi karin bayani
Legit.ng dai zata iya tuna cewa tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara Kanal Dasuki a ranar 15 ga watan Junin shekarar da ta gabata ta 2016 ya fadi warwas a kotun daukaka karar dake a garin Abuja bayan da ya bukaci a tursasawa shugaba Buhari ya sake shi.
Haka ma dai mai sauraro zai iya tuna cewa ana cigaba da tsare mai ba shugaban kasar shawara ne dai bisa ga umurnin gwamnatin tarayya biyo bayan tuhumar sa da ake yi da laifin yin facaka da kudaden kasa da suka tasar ma dala biliyan 2.1 na sayen makamai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng