Matsalolin Al'ummar Arewa: Jefar da jarirai a bola, laifin waye?

Matsalolin Al'ummar Arewa: Jefar da jarirai a bola, laifin waye?

A kullum sai anji labarin cewa an tsinci jariri a bola ko a kwali an yar, ko an jefar a shadda, ko an kashe, ko an gudu an bari. Da gani dai masu gudun abin kunya ne ke wannan aika-aika, wadanda suka rasa yadda zasu yi da cikin da suka yi kafin aure. Ina mafita?

Matsalolin Al'ummar Arewa: Jefar da jarirai a bola, laifin waye?

Matsalolin Al'ummar Arewa: Jefar da jarirai a bola, laifin waye?

Al'adu da addini na yankin mu na Arewa, akwai kunya, akwai kara, akwai kawaici, akwai kuma tarbiyya, da sanin ya-kamata. Sai dai kuma, al'ummar cike take da gulma, da sa-ido, da kiwon mutane, da fasikanci, na boye, da son nuna laifin wani da boye naka.

Arewa dai ta ki gaya wa kanta gaskiya, sai kunya da nuqu-nuqu, an ki wayar da kan jama'a kan harkkin saduwa ta jima'i, da kiwon lafiya, da kare kai daga cututtuka da ma harkokin ciki. Kowa na gani abin kunya ne ya zauna ya ko ta tauna batun jima'i da 'ya'ya, maza da mata, musamman budurwai.

DUBA WANNAN: Shin Janar Abacha barawo ne ko kuwa a'a?

A duk fadin duniya dai, ana koyar da yara sanin ilimin jima'i, babu kunya a ciki, amma arewa tayi kekas ta hana, da sunan al'ada da addini, sai dai a bar yaro ko yarinya su koya a wurin abokai, ko a talabijin, ko a hanyoyin batsa, wanda hakan ke kai ga lalacewa.

Idan da 'yan mata da yawa sun sami fuskar tambaya ko ilimi ko kai kukansu wurin iyayensu, musamman mata, da da yawa basu fada tarkon karuwanci, ko tsautsayin soyayyar da zata kai ga saduwa ko ffyade ba, ko ma ciki.

Sanin yadda mutum zai kare kansa daga cututtuka na zamani, zai iya kiyaye da yawa daga hadurra. Karyane ace wai ai don anyi wa'azi, kowa zai kame kansa, lokacin balaga, duk wanda ko wadda ta sami dama, zasu so su ji me jikinsu yake bukata, da yawa kuma hankalinsu bai kai ga su yi aure ba ko su rike iyali.

Hanyoyin saduwa da jima'i ba tare da abin kunya ba, da kuma kare kai daga cutuka, da ma hanyoyin kula da kai, duk an barwa abokai da kawaye, da hanyoyin sadarwa, iyaye sunyi tsit, ko ma suma suna yi tasu barikin a boye.

Ga matsalar auren wuri, da ma fitowa daga auren a shekaru kanana, wanda tuni ya koyawa yarinya saduwa da namiji, da dadin hakan, wanda kuma talauci kan jefa ta neman na katin waya da kayan kwalam, su kuwa samari, kamar sa ci da gashi, duk ko ina sun baza komarsu.

A yanzu lokaci ne da iyaye zasu zauna su iya baiwa 'ya'yansu fuska, ta yadda jikin su yake, da yadda rayuwa take, ba boye-boye, da kuma karbar kokensu ba tare da tozartawa ko kunyatawa ko azabtarwa ba, idan abin tsautsayi ya abku.

Al'umma kuwa, dole su daina gulma da zunde da sa ido, kan 'yar wane ko wace tayi cikin shege, tayi abin kunya. Ke kuma uwa, dole ki rungum 'yarki ki so ta koda ta yi abun kunyar, saboda shirunki a baya ya hana ta ganewa, har ta kai ga hakan.

Ke kuma budurwa, danki, ko 'yarki, ko ta aure, ko ta soyayya, kai koma ta fyade ce, muddin kika haife, to fa jariri basshi da zunubi, kuma ko da lahira ko babu, da dai rai ne, kula dashi ya zama dole. Ki cije ko duniya zata qi ki, ki rike danki ko 'yar ki, kar ki yar a bola.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel