Jiragen ruwa sun iso bakin tekun Legas cike da man fetur

Jiragen ruwa sun iso bakin tekun Legas cike da man fetur

- Manyan jiragen ruwa 3 cike da man fetur sun iso tekun Legas

- Mai Kanti Baru yayi alkwarin cewa ba za a yi wahalar man fetur a lokacin bikin Krimeti ba

- Jihohi 11 tare da birnin tarayya sun fara wahalar ma

A yammacin talata 5 ga watan Disamba jiragen manyan ruwa guda 3 suka iso tekun Legas cike da man fetur.

Kamar yadda shugaban ma’aikatar man fetur (NNPC) Mai Kanti Baru ya sanar na cewa ba zai ayi wahalar mai ba duk da yada jita-jitar da ake yin na cewa zai ayi wahalar mai kasar.

Mai kanti Baru yayi alkwarin cewa ba za ayi wahalar mai ba a lokacin bikin krismeti a watan Disamba.

Jiragen ruwa sun iso bakin tekun Legas cike da man fetur
Jiragen ruwa sun iso bakin tekun Legas cike da man fetur

Bayan haka hukuma kula da iyakokin ruwa NPA sun ce akwai sauran jiragen guda 26 dauke da man fetur da kayan abinci da ake sa ran za su iso kasar daga ranar Talata zuwa 30 ga watan Disamba na shekara 2017 da muke ciki.

KU KARANTA : 2019 : Atiku ba zai iya ka da Buhari ba – Tony Momoh

Legit.ng ta samu rahoton yadda jihohi guda goma 10 tare birnin tarayya Abuja suka fara wahalar mai saboda jitar jitar karanci mai da aka ta yadawa a gari.

Wasu jihohin sun fara sayar da litar daya farashi 160.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng