Zargin maita: Mafusatan matasa sun kashe, tare da kona wani hedimasta

Zargin maita: Mafusatan matasa sun kashe, tare da kona wani hedimasta

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa wasu mafusatan matasa a kauyen Nneoche dake a karamar hukumar Mbano, jihar Imo sun kashe tare da kone gawar wani shugaban makarantar Furamare bisa zargin sa da ake yi da maita.

Mun samu dai cewa Hedimastan mai suna Mista Cosmas Nwaiwu mai shekaru 57 a duniya ya gamu da ajalinsa ne a ranar Laraba, 27 ga watan daya gabata sannan kuma jim kadan da kisan nasa is matasan suka cinnawa gawar sa wuta.

Zargin maita: Mafusatan matasa sun kashe, tare da kona wani hedimasta
Zargin maita: Mafusatan matasa sun kashe, tare da kona wani hedimasta

KU KARANTA: Kalaman Atiku na farko bayan ziyartar ofishin PDP

Legit.ng dai ta samu cewa an dai dade ana zargin Hedimanstan da yin maita tare kuma da lalata rayuwar wasu yara 2 'yan uwan sa tare da lashe wasu mutanen da dama.

Jami'in hulda da jama'a dai na rundunar 'yan sandan jihar Mista Andrew Enwerem ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kuma bayyana cewa tuni sun kama matasan da ake zargi da aikata hakan sannan kuma ana cigaba da bincike.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng