Lafiya Uwar Jiki: Anfanin kafar kaza 4 a jikin dan adam da zasu baku mamaki
Tabbas dukkan dan adam yana bukatar abinci mai gina jiki da kuma zai kara masa lafiya da karsashi a yayin rayuwar sa ta duniya kafin ya koma ga mahallicin sa.
Cikin abubuwan da dan adam kan yi sha'awar ci akwai na man dabbobi da tsuntsaye a ciki da suka hada hadda kaza to sai dai ba kowa ne ke cin kafar kaza ba idan an yanka da yawa daga cikin mutane sukan yadda ta ne.
Legit.ng kamar yadda muka saba yauma mun tattaro maku kadan daga cikin anfanin kafufun kaza a jikin dan adam:
1. Kafar kaza tana kara lafiyar kashi tare da kare jiki daga manyan ciwukan kashin irin su ciwon gabobi da sauran su.
KU KARANTA: Anfani zogale 18 a jikin dan adam da baku sani ba
2. Haka ma dai bincike ya nuna cewar kafar kaza na magance matsalar nan ta saurin tsufa da wuri.
3. Haka zalika kafar kaza kamar dai yadda muka samu tana magance saurin hauhawar jini musamman ma ga masu matsalar ta hawan jini.
4. Kafar kaza tana da matukar anfani wajen kara karfin kashi, lafiyar jijiyoyi da kuma kwarin hakora da ma akaifa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng