Rayuka 5 sun jigata sanadiyyar kazamin fadan fulani da 'yan kabilar Berom
Labaran da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa yanzu haka an samu tabbacin mutuwar mutane akalla 5 sanadiyyar kazamin fadan da aka gwabza tsakanin Fulani da kuma 'yan kabilar Beron a wajen wani hakar ma'adanai a kauyen Rafin Acha, karamar hukumar Riyom ta jihar Filato.
Majiyar mu da ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata kwana daya bayan da aka zargi wasu fulani da shigar da shanun su cikin gonar wani dan kabilar Berom.
KU KARANTA: Saukin kai gare ni - Jaruma Nafisa Abdullahi
Legit.ng dai ta samu a sanadiyyar hakan ne wasu matasan kabilar ta Berom suka far wa wasu fulanin lamarin da ya yi sanadiyyar kazamin fada a tsakanin kabilun biyu.
Shugaban rundunar wanzar da zaman lafiya ta Operation Safe Heaven, Kaftin Umar ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan kuma ya kara da cewa wasu matasan 5 da suka hada da 'yan kabilar Beron 4 da ba fullatani 1 sun samu mummunan rauni.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng