Aisha Buhari tayi ma Najeriya addu’a a Masallacin Annabi dake Madina (Hoto)
- Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta tafi Umarah
-Aisha Buhari ta taya Najeriya addu'a samun zaman lafiya
Uwargidar shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta taya Najeriya addu’ar samun zaman lafiya, hadi kai, karuwar ariziki da kuma cigaba mai daurewa, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Mai dakin shugaba Buhari, ta yi wannan addu’a ne a ranar Juma’a 1 ga watan Nuwamba a masallacin Annabi Muhammadu (SAW) a yayin ziyarar Ummara da ta kai.
KU KARANTA: Wasu Iyaye sun daka ma wata Malama dukan kawo wuƙa a kan ta zane ɗalibarta, har ta mutu
Uwargida Aisha ne da kanta ta daura hoton nata yayin da take karatun Al-Qur’ani a shafinta na kafar sadarwar zamani, wato Facebook a yau Juma’a.
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yau Juma’a 1 ga watan Disamba, wanda yayi daidai da 12 ga watan Rabiul Auwal a matsayin ranar hutu a Najeriya don bikin Maulidi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng