An gano kayataccen hotunan Zahra Buhari-Indimi a wajen wani biki a Abuja
An gano kyakkyawar yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Buhari Indimi cikin hadewa kwanan nan.
Uwargidan Indimi ta halarci wani taro ne tare da mai daukar mahaifinta hoto na musamman, Bayo Omoboriowo wanda aka gudanar a Abuja kwanan nan.
Legit.ng ta tuna cewa Zahra da maigidanta sunyi aure a watan Disamban 2016 sannan kuma an gano ma’auratan a gurare da dama inda suke nuna ma junansu so da kauna.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya gaza a dukka alkawaran sa - Briggs
Kwanaki Zahra ta janyo cece-kuce a yanar gizo bayan ta kaddamar da cewa mijinta wanda ya kasance biloniya, Ahmed Indimi, yayi kama da marigayi shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha.
Ga karin hotuna a kasa:
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng