Jerin Kasashe 32 da zasu fafata a gasar kwallon kafa ta kofin duniya
Legit.ng ta kawo muku jerin kasashen 32 da suka yi nasarar samun damar fafatawa a gasar kwallon kafa ta kofin duniya da za a kara a kasar Rasha a shekarar 2018.
Kasar Samba wato Brazil itace kasa ta farko da ta fara samun cancantar karawa a gasar kwallon kafa yayin da kasar Peru ita ce kasa ta karshe da samu cancantar karawa a gasar bayan ta lallasa kasar New Zealand.
Ita ma kasa Najeriya ba a barta a baya, domin kuwa ita ce kasa ta 12 da ta samu cancantar karawa a gasar da za a fafata a kasar Rasha, bayan ya rage mata sauran wasa guda na neman cacanta, inda ta buga wasanta na karshe da kasar Algeria a birnin Constantine wanda ya zamto ci banza bari banza.
Ga jerin kasashe 32 da su fafata a gasar kwallon kafa ta kofin duniya tare da nahiyyar kowace kasa:
Nahiyyar Asia - Iran, Japan, Koriya ta Kudu, Saudiya da Australia.
Nahiyyar Afirka - Najeriya, Masar, Senegal, Morocco da Tunisia.
Nahiyyar Amurka ta Arewa - Mexico, Costa Rica da Panama.
Nahiyyar Amurka ta Kudu - Brazil, Argentina, Columbia, Uruguay da Peru.
Nahiyyar Turai (Europe) - Rasha, Belgium, Jamus, Ingila, Andalus, Poland, Iceland, Serbia, Faransa, Portugal, Switzerland, Croatia, Sweden da Denmark.
KARANTA KUMA: Maikanti Baru ya zama gwarzon shekarar 2017 a bangaren man fetur da gas na nahiyyar Afirka
Legit.ng ta ruwaito a makon da ya gabata cewa, Kaftin din 'yan kwallon Najeriya ta Super Eagles, John Mikel Obi, ya bayyana farin cikin sa sakamakon nasarar da suka yi a wasan sada zumunta da kasar Argentina, inda suka tashi 4-2 a kasar Rasha.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng