Wani Mahaukaci ya sassara wasu ƙananan Yara ýan Firamari, amma fa ya gamu da gabansa
Wani mutumi da aka bayyana shi a matsayin mai tabin hankali, Gaji Adamu yayi amfani da adda ya daddatsa wani kananan yara su biyu yan makarantar Firamarin Jafi dake cikin Karamar hukuma Kwaya Kusar.
Daily Nigerian ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar Borno, Victor Isuku yace baya da daliban biyu daya kashe, ya raunata wani Malami guda, tare da wata daliba.
KU KARANTA: Mugun baƙo, daga zuwa baƙunta ya tattara talabijin guda 120 ya cika wandonsa da iska
“Da misalin karsfe 9:30 na safiyar ranar ALhamis, 30 ga watan Nuwamba, wani mutum Mahaukaci mai suna Gaji Adamu ‘Male’ a garin Kwaya Kusar ya kutsa makarantar Firamrin Jafi dauke da adda, inda ya kashe dalibai biyu tare da jikkata Malami da daliba.” Inji Isuku.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin ya bayyana cewa ganin haka ya sanya wasu fusatattun matasa suka diran masa, suka lakada masa dan ban zan duka, wanda a yanzu haka yana hannun Yansanda, sun mika shi ga Asibiti.
Sai dai kwamishinan Yansandan jihar, Damian A Chukwu ya sa an mika gawarwakin daliban zuwa babban asibitin garin Gombe, sa’annan ya bada umarnin a fara gudanar da bincike akan mutumin don tabbatar da matsayin hankalinsa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng