Makami daya zamu harba mu rusa Amurka gabadayan ta - Koriya ta Arewa

Makami daya zamu harba mu rusa Amurka gabadayan ta - Koriya ta Arewa

Kasar Koriya ta Arewa ta ce yanzu haka ta mallaki wani makamin kisan kare dangi na Nukiliya mai linzami, ICBM, da zai iya tashin kasar Amurka gabadayan ta daga aiki.

Kasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamin mai samfurin Hwason-15 ne aranar Laraba da sassafe tare da bayyana farincikin ta bisa cimma burin ta na mallakar makamin mai linzami.

A yanzu haka dai majalisar dinkin duniya ta kira wani taron gaggawa domin tattauna matakin da ya kamata a dauka a kan kasar Koriya ta Arewa biyo bayan saba dokar kasa da kasa da tayi ta hanyar yin gwajin makamin mai linzami.

Makami daya zamu harba mu rusa Amurka gabadayan ta - Koriya ta Arewa
Makami daya zamu harba mu rusa Amurka gabadayan ta - Koriya ta Arewa

Gwajin makamin mai linzami da kasar Koriya ta Arewa ta yi, ya sabawa takunkumin da majalisar dinkin duniya ta yi a kan mallakar makami mai linzami.

DUBA WANNAN: Yariman daular Birtaniya Harry na shirin auren bakar Amurka

Makamin yayi tafiya mai nisan kilomita 4,475, nisan da wani makami mai linzami bai taba yi ba, kafin daga bisani ya dira a tekun kasar Japan.

Koriya ta Arewa ta sha ikirarin cewar zata iya kaiwa Amurka hari da makami mai linzami amma sai yanzu ne ta tabbatar da hakan bayan gwajin makamin na jiya.

Hakazalika wasu masana makami mai linzami sun tabbatar da cewar makamin zai iya kaiwa kasar Amurka saidai sun bayyana cewar ba zai iya daukan makamai masu yawa ba matukar zaiyi nisan zango.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng