Tsohon matamakin shugaban kasa Atiku Abubakar dan siyasa ne mara Akida da alqibla - Agoro
- Dakta Olapade Agoro ya kwatanta Atiku a matsayin dan siyasa mara Akida da Alqibla
- Olapade ya ce shi ba ga dalilin da zai sa Atiku ya bar jam'iyyar APC ba
- Da Atiku mutumin kirki ne kuma mai gaskiya ba zai taba fita daga APC ba inji dakta Olapade
Tsohon dan takarar kungiyar NAC, dakta Olapade Agoro ya kwatanta tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan siyasa mara akida da alqibla.
Dakta Olapade Agoro yace “da Atiku a tsaya a jam’iyyar APC an gyara duk matsalolin da kasar ke fuskanta da ya fi masa.
Ba wai ya saba alkwarin da yayi ba na cewa ba zai taba fita daga jam’iyyar APC ba.
KU KARANTA : Buhari ne ya sa ministan Shari’a ya tattauna da ni sannan ya tabbatar da dawo dani bakin aiki – Inji Maina
Dakta Olapade Agoro ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da yan jarida a Ibadan, yace bai ga wani dalili da zai sa Atiku ya bar jam’iyyar APC ba.
Idan Atiku dan siyasa kirki ne kuma mutum ne mai gaskiya, ba zai taba ficewa daga jam’iyyar APC ba, saboda shi da kanshi ya ce APC ne jam’iyyar shi na karshe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng