Shugaban kasar Kwadebuwa ya tarbi Buhari da tawagarsa a Abidjan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Abidjan na kasar Kwadebuwa da yammacin ranar Talata 28 ga watan Nuwamba don halartar taron kasashen Afirka da na nahiyar Turai.
Shugaba Buhari tare da tawagarsa sun samu tarba daga hannun shugaban kasar, Alassa Outtara, wanda ya kwashe lokaci yana jiransu a filin sauka da tashin jirage na Abidjan.
KU KARANTA: Ke Duniya: Yadda wasu Yara 2 suka kai ma Mahaifinsu hari da nufin halaka shi
A yayin taron, ana sa ran Buhari zai gana da wasu shuwagabannin kasashen Turai da na Afirka akan batutuwan da suka shafi cigaban Najeriya da ma na sauran kasashen.
Twagar shugaba Buhari ta kunshi jagoran jam’aiyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, gwamnan jihar Akwa Ibom Emmanuel Ortom, da gwamnan jihar Bauchi, M.A Abubakar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng