Taron PDP a Kaduna: An tashi baram-baram saboda kin ambatar sunan Sule Lamido
- An yi kare jini biri jini a taron PDP a Kaduna saboda kin ambaton Sule Lamido
- Wasu masoyan Lamido sun zargi an shirya taron PDP ne kawai domin wata manufa, amma ba domin ci gaban jam'iyyar ba
- Jerry Ghana ya ambato sunayen wasu jigon jam'iyyar wadanda ya ce tarihi ba zai manta da su ba
Hayaniya ta barke a taron jam'iyyar adawa ta PDP shiyyar arewa maso yammacin kasar wanda aka gudanar a Kaduna, biyo bayan kememe da daya daga cikin jiga-jigan PDP, Farfesa Jerry Ghana ya yi na kin ambaton sunan tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a PDP, Alhaji Sule Lamido.
Lamido ya kasance daya daga cikin manyan masu sha'awar neman shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa na 2019 a karkashin jam'iyyar PDP.
A taron Farfesa Jerry Ghana ya ambato sunayen wasu jigon jam'iyyar wadanda ya ce tarihi ba zai manta da su ba, sakamakon gudumuwar da suka bayar wajen ciyar da jam'iyyar gaba, inda ya ambaci irin su Mista Solomon Lar da Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Bafarawa da Jonathan da kuma Obasanjo, a matsayin wadanda suka bayar da gudummuwa wajen inganta PDP a Najeriya.
Har Ghana ya kammala sunayen manyan 'ya'yan jam'iyyar bai kira sunan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ba, lamarin da ya tunzura wasu mahalarta kuma masoyar Lamido a taron ke nan, suna ganin cewa an shirya taron ne kawai domin wata manufa, amma ba domin ci gaban jam'iyyar ba.
KU KARANTA: Bikin cika shekara 61 da haihuwar Kwankwaso
Wasu daga cikin mahalarta taron, sun shida wa majiyar Legit.ng cewar babu gyara akan tsarin tafiyar jam'iyyar a yanzu, kuma za'a iya samun matsala babba a tafiyar matukar ba'a dauki matakan da suka dace ba, domin kamar yadda suka bayyana cewa da gangan ne Jerry Ghana ya ki ambaton sunan Sule Lamido a tafiyar PDP, amma ya ambato sunan Ibrahim Shekarau wanda ya shigo PDP da rana tsaka.
Idan baku manta ba, a karshen makon nan ne tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Sule Lamido ya tara dubban mutane a garin Ringim inda wasu suka ce ba shakka za a buga da shi a wajen neman kujerar shugaban kasar a zaben shekara ta 2019. Lamido yana cikin wadanda su ka ki barin jam’iyyar PDP.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng