Rikicin Sanata Misau da shugaban 'yan sanda: Gwamnatin tarayya ta nemi sasanci
Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta shigo tsakanin rikicin nan da yaki ci-yaki cinyewa dake ke tsakanin Sanata Isah Hamman Misau na jihar Bauchi ta tsakiya da kuma shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris.
Majiyar mu dai dake a kusa da gwamnatin ta bayyana mana cewa gwamnatin tarayyar ta kuduri aniyar sasanta dukkan bangarorin domin kaucewa dukkan wata baraka da ka iya shiga tsakani da kuma zata iya ba 'yan adawa dama don suyi gwamnatin dariya.
KU KARANTA: An bukaci Shugaba Buhari ya kori Malami
Legit.ng dai ta samu cewa tuni dai kwamitin da gwamnatin tarayyar ta wakilta ya sasanta su din ya nemi bangarorin da su sasantanta kansu ba tare da anje kotu ba.
Mun samu dai cewa kadan daga cikin shirye-shiren sasanta su din tuni Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya tsara wani muhimmin taro tare da dukkan bangarorin biyu domin lalubo bakin zare.
Mai karatu dai zai iya tuna dangantaka tayi tsami a tsakanin bangaren na majalisar dattijai da kuma hukumar 'yan sandan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng