Shugabannin da suka kafa PDP a APC za su dawo ba da daɗewa ba - Inji Bode George
- Tsohon mataimakin shugaban PDP ya ce da sauran manyan jam’iyyar APC da zasu dawo PDP
- George ya gargadi jagorancin jam'iyyar PDP akan musayar ‘yan takarar jam’iyyar
- George ya ce akwai sauran jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar APC da yawa da zasu dawo
Bode George, jigo na jam'iyyar PDP, kuma dan takarar shugabancin jam’iyyar, ya yi ikirarin cewa wasu shugabanni da suka kafa PDP wadanda a halin yanzu suna jam'iyyar APC, za su dawo kamar yadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi.
Tsohon mataimakin shugaban jam’yyar na PDP ya ce hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a Katsina a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba.
Legit.ng ta tattaro cewa, George kuma ya gargadi jagorancin jam'iyyar ta yadda ba za a musayar kowa ba domin jam'iyyar ta kasance ga dukkan 'yan Najeriya.

Ya ce: "Yayin da gidanka yake yoyo, shin za ka yi watsi da ita ne ka koma zama dan haya?”
KU KARANTA: 2019: Sharuddan da Atiku zai cika kafin mu ba shi Takara – Walid Jibrin
"Za ka gyara kuma ka zauna a gidan saboda kai maigidan ne. Domin idan ka kasance mai haya a ko'ina, mai gida zai iya fitar da kai a kowane lokaci”.
'' Saboda haka, yana ƙoƙari ya dawo gida, gidan da suka gina, gidan da suka kasance sune tushen ta. Akwai sauran jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar da yawa da zasu dawo. Bari su zo”, inji shi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng