Dandalin Kannywood: Ku kallin kayatattun hotunan jaruma Halima Atete na bikin cika shekara 29
A jiya Lahadi ne dai kamar yadda muka samu daga bakin Jarumar, 26 ga watan Nuwamba, Halima Atete ta cika shekaru 29 a duniya sannan kuma shekaru da dama kenan ana ta damawa da ita a harkar shirya fina-finai a masana'ar Kannywood.
Jarumar dai a wani irin salo na kasauta ta shirya mashahurin bukin walimar cin abinci ne inda masoyan ta da ma 'yan uwa da abokan arziki suka ci suka kuma sha duk domin nuna farin cikin nasu da zagayowar haihuwar tata.
KU KARANTA: Dalilin da yasa mijina ya sake ni - Jaruma Asma'u
Legit.ng dai ta samu cewa kawunan jama'ar gari musamman ma masu sha'awar fina-finan na hausa dai sun rarraba wajen amincewa ko rashin amincewar su game da ainihin hakikanin shrkarun jarumar na gaskiya inda wasu da dama ke kallon ta fi haka a shekaru.
A yayin bikin walimar cin abincin dai jarumar ta godewa Allah da ya rayata ya kuma yi maa ni'ima ta mutane da daukaka sannan kuma ta sha alwashin ci gaba da nishadantar da al'umma masoyanta.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng