Nigerian news All categories All tags
Yaudara: Wata mata ta gano mijinta mai wankin mota ne ba mai sayar wa ba watanni 4 bayan aure

Yaudara: Wata mata ta gano mijinta mai wankin mota ne ba mai sayar wa ba watanni 4 bayan aure

Lallai al'amarin duniya da yawa yake sannan kuma abun al'ajabi ko dariya baya karewa idan dai mutum na numfashi a doron kasar. Kuma tabbas ko shakka babu irin karairayin da samari da 'yan mata ke yi wa junan su abun takaici ne matuka.

Nan ma dai labarin wata yariya 'yar shekara 25 a duniya ce da ta gano mijin ta da ta aure na wata hudu mai sana'ar wankin mota ne ba wai mai saye-da-sayar wa ba kamar yadda ya fada mata kafin auren.

Yaudara: Wata mata ta gano mijinta mai wankin mota ne ba mai sayar wa ba watanni 4 bayan aure

Yaudara: Wata mata ta gano mijinta mai wankin mota ne ba mai sayar wa ba watanni 4 bayan aure

KU KARANTA: Atiku na cigaba da ganawa yan jam'iyyar PDP

Legit.ng ta samu dai cewa matar, a cikin kukan zuci da nadama ta bayyana cewa a yayin da suke ta tsula soyayyar su kafin aure kullum yakan zo mata da motoci ne kala-kala da kuma yake ce mata saida su yake yi a matsayin sana'a wanda hakan ne ma yasa ta amince ta aure shi.

Zankadediyar budurwar dai ta nuna matukar nadamar ta akan hakan sannan kuma ta nemi jama'a da su bata shawarar yadda zata bullowa lamarin don kuwa ta riga ta shiga tarkon samarin zamani.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel