Nigerian news All categories All tags
Neman Taimakon Al’umma: Mallam Lawali Ahmad Anka na fama da cutar koda

Neman Taimakon Al’umma: Mallam Lawali Ahmad Anka na fama da cutar koda

- Mallam Lawali Ahmed Anka yana bukar taimako daga al’ummar kasar akan cutar koda da yake fama da shi

- Allah ya jarabi mallam Anka da ciwon koda tsawon sama da shekara daya yana jinya

- Yanzu haka ana bukatar miliyan 8 a asibiti don a dasa masa koda

Lawali Ahmed Anka, Malami ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya dake Kauran Namoda, jihar Zamfara. Allah ya jarabce shi da ciwon koda tsawon sama da shekara daya yana jinya. Duk abinda ya ke da shi ya kare.

Kamar yadda Legit.ng ta samu daga shafin Zuma Times Hausa, abokan aikinsa sun tallafa masa da kudi naira miliyan 3, amma duk da aka sun kare gaba daya wajen neman magani. Yanzu haka an kai shi asibitin da za a dasa masa koda a kan naira miliyan 8 wanda kuma tafi karfin malamin.

Don haka ana kira ga gwamnatin jihar Zamfara ko 'yan siyasar yankinsa ko wani mai hali da su taimaka su dauki nauyin wannan dattijo, domin ceto rayuwarsa.

Neman Taimakon Al’umma: Mallam Lawali Ahmad Anka na fama da cutar koda

Lawali Ahmed Anka, malamin kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya dake Kauran Namoda

KU KARANTA: Maryam Sanda: Ashe Bilyaminu ba yaron tsohon Shugaban PDP bane

Allah ya ba da ikon taimakawa.

Neman Taimakon Al’umma: Mallam Lawali Ahmad Anka na fama da cutar koda

Takadar asibiti

Neman Taimakon Al’umma: Mallam Lawali Ahmad Anka na fama da cutar koda

Lambar asusun ajiye kudi na mallam Lawali Ahmed Anka

FIRST BANK ACCOUNT

Lawal Ahmed Anka

Account number: 3108344861

Don neman karin bayani za a iya tuntubi Abdulmalik Sa'idu mai Biredi, sakataren watsa labarai na kungiyar Muryar Talaka Na Jihar Zamfara kan lambar waya: 08069807496.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel