Buhari ya sake ware Naira biliyan 28 don baiwa jahohi 35 tallafi

Buhari ya sake ware Naira biliyan 28 don baiwa jahohi 35 tallafi

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta amince da ba jahohin kasar nan 35 a cikin 36 da ke garemu wani sabon tallafin bashin da yakai akalla Naira biliyan 28 da ya kama kusan Naira miliyan 800 domin cike gibin kasafin kudin su da suka kuduri aniya don biyan albashi da sauran nauye-nauyen dake a bisa kan su.

Babban minista a ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare mai suna Udoma Udoma shine ya sanar da hakan a yayin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa jiya Alhamis jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tattalin arziki karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Buhari ya sake ware Naira biliyan 28 don baiwa jahohi 35 tallafi
Buhari ya sake ware Naira biliyan 28 don baiwa jahohi 35 tallafi

KU KARANTA: Buhari zai sake farfado da shingayen karbar haraji

Legit.ng ta samu cewa Udoma ya bayyana cewa tuni ma ministar kudi Uwar gida Kemi Adeosun da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele suka kammala tsare-tsaren hakan tare kuma da bayar da umurnin baya jahohin kudaden.

Haka ma dai da yake karin haske game da batun, Udoma ya kara da cewa shi ma dai babban akawun gwamnatin ta tarayya har ya samu umurnin yin hakan sannan kuma ya tanbbatar da cewa jihar Legas ce kawai ba zata karbin kudin ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng