Lafiya jari: Hanyoyi 4 na magance tumbi mafi sauki da baku sani ba

Lafiya jari: Hanyoyi 4 na magance tumbi mafi sauki da baku sani ba

Hakika katon tumbi sifa ce mummuna kuma marar kyau a dukkan jinsin mace ko namiji musamman ma kuma ganin yadda katon tumbin yake da alaka da cututtuka da dama ga lafiyar sa.

Legit.ng ta tattaro maku wasu muhimman hanyoyi masu saukin gaske da zaku kawo karshen tumbin ku.

1. Barin shan giya

Hakika giya itace uwar dukkan zunubbai kamar yadda yake a addinin Islama, haka nan ma kuma shan giyar yana tattare da tarin cututtuka marasa adadi da misali ciki kuwa hadda yin katon tumbin. Barin shan giya yana magance tumbi.

Lafiya jari: Hanyoyi 4 na magance tumbi mafi sauki da baku sani ba
Lafiya jari: Hanyoyi 4 na magance tumbi mafi sauki da baku sani ba

KU KARANTA: Rundunar 'Yan sanda ta nemi kotu ta yankewa matar Bilya hukuncin kisa

2. Cin abinci dai-dai kima

Haka ma dai cikin abubuwan da ke sa dan adam yin tumbi hadda yawan cin abincin da ya wuce kima domin kuwa yin hakan yakan kara budawa mutum tumbin sa.

Ko shakka babu cin abinci dai-dai misali yakan magance wannan matsalar.

3. Rage cin abinci mai bada kuzari

Kamar yadda aka sani a kimiyyar likitanci akwai nau'ukan kayayyakin abinci kala-kala ciki hadda nau'in da ke sa kuzari.

Yawan cin abinci mai sa kuzari kadai ba tare da sauran nau'oin ba kan tilastawa jikin sarrafa shi ya zuwa wani nau'in kuma yana ajiye shi a jikin tsokar tumbi.

Don haka cin abincin da ya kunshi dukkan nau'oin sinadarai kan kawo karshen wannan matsalar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng