Manya manyan jiragen ruwa guda 4 sun nufo jihar Legas ɗauke da man fetur
Akalla jiragen ruwa hamshakai guda hudu ne ke tafe daga kasashen Turai suka iso kasa Najeriya, dauke da kayayyakin abinci da kuma man fetir a ranar ALhamis 23 ga watan Nuwamba.
Jiragen sun sauka ne a tashar jirgin ruwa dake jihar Legas, kamar yadda hukumar kula da tashoshin jiragin ruwan Najeriya, NPA, ta bayyana cikin wata sanarwa data fitar.
KU KARANTA: Kuma dai: Wani matashi ya luma ma abokinsa wuka a sanadiyyar caca
Legit.ng ta ruwaito sanarwa ta kara da cewa ana tsammanin jiragen talatin da uku makare da kayan abinci da kuma man fetir zasu shigo Najeriya daga ranar Alhamis 23 ga watan Nuwamba zuwa ranar 23 ga watan Disamba.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito baya da abinci da man fetur, jiragen na dauke da filawa, sundukai, kayan yan kasuwa, man gas da kuma man jiragen sama.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng