An yi yinkurin yiwa shugaba Buhari juyin mulki
Ta bayyana cewa, wasu magoya baya na gidi na tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, sun so a juyin mulki domin hana shugaban kasa Muhammadu Buhari darewa kujerar shugabancin kasar nan.
Bayan da Jonathan ya amince da nasarar zaben shugaba Buhari a shekarar 2015, an kawo wani yunkuri da soji za suyi juyin mulki a kasar nan, wanda zai hana Jonathan ko Buhari shugabantar kasar nan.
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan yunkuri yazo ne sakamakon fargaba da wasu jiga-jigan kasar nan suka yi na cewa, Buhari zai yi ramuwar gayya kan wadanda suka yi mishi danwaken zagaye a lokacin zabe.
Sai dai wani mutum guda da ba a bayyana sunan shi ba, ya dakatar da wannan manufa ta juyin mulki, da cewar ta faru ta kare, domin in har juyin mulki zai yi wani tasiri to kafin a gudanar da zabe ne, amma yanzu bakin alkalami ya riga da ya bushe.
A yadda ruwayar wani littafi da Bolaji Abdullahi ya wallafa akan yadda Jonathan ya samu kuma ya rasa mulkin Najeriya wato "On a Platter Of Gold: How Jonathan Won and Lost Nigeria".
Kamar yadda marubucin littafin ya bayyana, "mutane da dama sun yi ajiyar zuciya yayin da suka saurari yadda ganawar Jonthan da Buhari ta kasance bayan an fadi sakamakon zabe inda Jonathan ya ce, ya mika wuya ga sakamakon kuma yana yiwa shugaba Buhari murnar wannan nasara da yayi."
"Wannan abu da Jonathan yayi, bai yiwa magoya bayan sa dadi ba, sakamakon rashin neman shawarar su kafin ya aikata hakan. Sai dai a wannan lokaci sun yi tunanin akwai wani tuggu da za su iya hadawa kafin a rantsar da shugaba Buhari."
KARANTA KUMA: Ba gudu ba ja da baya akan hukumomin DSS da NIA - Magu
"Cikin gaggawa wadannan mutane suka shirya zaman ganawa da juna domin kalubalantar lamarin, inda suka gano cewa ai bakin alkalami ya bushe, duk abinda za suyi yanzu zai zamto ihu ne bayan hari, domin kuwa a lokacin da aka dage lokacin zabe zuwa makonni 6, ya kamata su sauke shugaban hukumar zabe ana wannan lokaci (farfesa Attahiru Jega), yadda soji za su samu damar kulla matakan tuggu."
"A yayin da suke kokarin kulla tuggu wanda zai hana Jonathan da Buhari shugabancin kasar nan, sai suka fahimci cewa ba za iya jurar zubar da jini da hakan zai janyo ba, wanda anan shirin na su ya fara warwarewa."
"Shugabannin jam'iyyar PDP a wannan lokaci sun shiga wani taro na gaggawa wanda a lokacin Ahmed Adamu Mu'azu shine shuagabn jam'iyyar na kasa, inda suka yi shawarar Adamu Mu'azu ya bayar da sanawa ta cewa, jam'iyyar bata lamunce da sakamakon zabe ba saboda haka a dunguma zuwa kotu."
"Nan da nan Adamu ya ce ina ba zai yiwu ba, domin kuwa baza a dauke shi mutumin banza ba, yana da mutunci da ya kamata ya kare. Ya kuma ce mutumin da ya fadi zabe kuma yayi na'am da sakamakon zabe da har ya kira shugaba Buhari yana taya sa murna ba tare da neman shawarar mu ba, saboda haka sai dai kawai mu rungumi kaddara."
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng