Jirgin ruwan sojin kasar Amurka na yaki ya kife a gabar tekun Japan

Jirgin ruwan sojin kasar Amurka na yaki ya kife a gabar tekun Japan

Ministan tsaron kasar Japan, Itsunori Onodera, ya tabbatar da afkuwar hatsarin, tare da bayyana cewar hukumar tsaron kasar Amurka ta shaida ma sa cewar matsalar inji da jirgin keda shi ta haddasa hatsarin, jirgin na dauke da mutane da dama.

Ma'aikatar tsaro a Amurka ta bayyana cewar anyi nasarar ceto mutum 11 daga cikin fasinjojin jirgin. Hakazalika hukumar ta bayyana cewar matsalar inji ce ta haddasa hatsarin jirgin.

Jirgin ruwan sojin kasar Amurka na yaki ya kife a gabar tekun Japan
Jirgin ruwan sojin kasar Amurka na yaki ya kife a gabar tekun Japan

Jirgin kirar C-2 ya yi hatsarin ne a tekun kasar Japan a hanyar sa ta zuwa kasar Philippines inda babban jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki yake.

DUBA WANNAN: An baiwa sojin Najeriya umarnin koyon yarukan Hausa, Igbo, da Yoruba cikin shekarar daya

Wannan shine karo na biyu cikin shekarar nan da jirgin ruwan kasar Amurka yayi hatsari a tekun kasar Japan. Kuma ko a watan Agusta na shekarar nan saida wani jirgin yaki na ruwa mallakar sojin Amurka yayi karo da wata tanka a gabar tekun kasar Singapore tare da kashe mutum 10.

Kasar Amurka na kara tura tura dakarun soji ya zuwa kasashen yankin Asiya masu makobtaka da Koriya ta Arewa tun bayan da dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng