Buratai ya baiwa Sojoji shekara guda dasu koyi manyan yarukan Najeriya

Buratai ya baiwa Sojoji shekara guda dasu koyi manyan yarukan Najeriya

Rundunar Sojin kasa ta umarci dukkanin Sojojinta dasu fara koyon manyan harsunan Najeriya guda uku, kamar yadda Kaakakin rundunar Birgediya SK Usman ya bayyana.

Premim Times ta samu kwafin sanarwar, inda SK yace an baiwa kowane Soja daga yanzu zuwa watan Disambar shekara mai zuwa, ya koyi wadannan yarukan.

KU KARANTA: Sabon bidiyo ya billo inda yan ta’addan Boko Haram suka kai hari ga sojojin Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito SK yana fadin amfanin jin yaruka daban daban a wajen soja, inda yace hakan zai kara dankon dangantaka tsakanin jami’an tsaro, saukaka alaka da fararen hula, da kuma samar da hanya mai sauki wajen tattara bayanai.

Buratai ya baiwa Sojoji shekara guda dasu koyi manyan yarukan Najeriya
Sojoji

Duk da cewa yaren Turanci ne yaren hukumar Soji, rundunar ta uamrci Sojoji su koyi yarukan da ba nasu ba guda na daban, ga duk wanda yak ware a yarukan Hausa, Ibo da Yarbanci, akwai karin alawus alawus da za’a yi masa.

Haka zalika ga masu bukatar shiga aikin Soja, kwarewa a manyan yarukan Najeriya na daya daga cikin abubuwan dubawa, da zasu baiwa mai nema daman samun aikin Soja.

Tun a da, inji SK, Rudunar Sojan kasa na da Sojoji wadanda suka kware a yaren Faransanci, Larabci, yaren Sifen, yaren Fotugal da kuma Swahili.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng