An baiwa sojin Najeriya umarnin koyon yarukan Hausa, Igbo, da Yoruba cikin shekarar daya

An baiwa sojin Najeriya umarnin koyon yarukan Hausa, Igbo, da Yoruba cikin shekarar daya

Hukumar sojin Najeriya ta umarci kafatanin jami'an ta da su koyi yarukan Hausa, Igbo, da Yoruba cikin shekara daya.

"Ba wai mun ce sai sun kware cikin dukkan yarukan ba, abinda muke so shi ne zuwa watan Disambar shekarar 2018 dukkan wani jami'in soji a ce zai iya fahimta tare da isar da sako cikin yarukan guda uku" inji kakakin hukumar, Birgediya janar Sani Kukasheka Usman.

An baiwa sojin Najeriya umarnin koyon yarukan Hausa, Igbo, da Yoruba cikin shekarar daya
An baiwa sojin Najeriya umarnin koyon yarukan Hausa, Igbo, da Yoruba cikin shekarar daya

Kukasheka ya kara da cewar samun ilimin yarukan uku zai taimakawa jami'an soji wajen mu'amalar su da abokan aikin su sannan da ragowar fararen hula.

DUBA WANNAN: Rikicin jami'an hukumar EFCC dana DSS: Jami'an EFCC sun janye daga filin-daga

Kukasheka ya bayyana cewar daga yanzu hukumar sojin zata ke bawa wadan da suka yarukan uku fifiko wajen daukan aiki, sannan ya kara da cewa koyon yarukan wani abu sabon tsari ne da hukumar ta kaddamar baya ga tsohon tsarin karfafa gwiwar jami'an su koyi yarukan Faransanci, Swahili, yaren Spain dana kasar Fotigal.

Kukasheka ya rufe da cewar har yanzu yaren turanci shi ne yaren gwamnatin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng