Dandalin Kannywood: Yadda 'yan sanda suka kama Nafisa Abdullahi a Otel da tsakar dare
Babban furodusa Jamilu Ahmad Yakasai ya sa 'yan sanda sun kama fitacciyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa Nafisa Abudullahi da tsakar dare a garin Katsina sannan kuma suka kaita Kano tare da kulle ta a bayan kanta na tsawon lokaci.
Mun samu dai daga majiyar mu ta mujallar fim cewa musabbabin rigimar ta su ta samu asali ne sakamakon jingine aikin fim din shi mai suna 'Mutuwar Aure' da jarumar Nafisa ta yi ta tafi sabgar gabanta ba tare da kuma wani dalili ba.
KU KARANTA: Wasu malaman makaranta sun sake faduwa jarabawa
Legit.ng ta samu dai cewa wannan ne ma dai ya harzuka shi inda har ya shigar da kara a kotu inda aka soma shari'a a tsakanin su amma kuma sai jarumar ta ki zuwa kotun don ta kare kanta, a bisa akasin haka ma sai kawai ta tafi Katsina yin wani wasan daban.
To daga baya ne sai kotun ta umurci jami'an 'yan sanda su bazama neman ta inda kuwa suka kamota a Katsina kafin daga baya su sasanta kansu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng