Jerin shuwagabannin Najeriya da suka yi zamani da Mugabe tsawon shekaru 37 da yayi a karagar Mulki

Jerin shuwagabannin Najeriya da suka yi zamani da Mugabe tsawon shekaru 37 da yayi a karagar Mulki

Ta tabbata rigimammen shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya bankwana da madafan iko a jiya Talata 21 ga watan Nuwamba, inda ya aika ma majalisar dokokin kasar da sakon sa na murabus.

Yayan majalisar dokokin kasar sun samu labarin murabus din Mugabe ne a daidai lokacin da suke zaman tattauna yiwuwar tsige shi daga kujerar shugaban kasar, sai ga shi ta zo musu da sauki.

KU KARANTA: Ta faɗi masa gasassa: Za’a naɗa mataimakin Mugabe, Mangagwa shugaban kasa

Sai dai Legit.ng tayi nazarin tsawon mulki da shugaba Mugabe yayi daga 1980 daya hau, tsawon shekaru 37 da ya kwashe yana dafe da madafan iko a kasar Zimbabwe, inda tayi duba ga yawan shuwagabannin Najeriya da suka yi zamani da Mugabe kuma suka shude suka barshi.

Jerin shuwagabannin Najeriya da suka yi zamani da Mugabe tsawon shekaru 37 da yayi a karagar Mulki
Mugabe da Obasanjo

1. Shugaba Shehu Shagari:

Alhaji Shehu Shagari ya mulki Najeriya tun daga 1 ga watan Oktoban 1979 zuwa 31 ga watan Disambar 1983, hakan ya nuna cewa Mugabe ya tarar da shi a kan mulki, amma Shagari ya wuce ya bar shi.

2. Muhammadu Buhari:

Manjo janar Muhammadu Buhari ne ya zamo shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, bayan hambarar da gwamnatin Shagari, daga 31 ga watan Disambar 1983 zuwa 27 ga watan Agusta 1985, shima ya buga ya bar Mugabe.

Jerin shuwagabannin Najeriya da suka yi zamani da Mugabe tsawon shekaru 37 da yayi a karagar Mulki
Mugabe da Buhari

3. Ibrahim Badamasi Babangida

Sai kuma janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda ya kwashe kusan shekaru takwasa yana mulki, daga 27 ga watan Agustan 1985 zuwa 26 ga watan Agustan 1993, shima ya wuce ya bar Mugabe yana nan daram dam dam.

4- Earnest Shonekan

Cif Ernest Shonekan ne ya zamo shugaban kasa bayan murabu sa IBB yayi, inda ya kwanaki 83 kacal a mulki, daga 26 ga watan Agustan 1993, zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993. A gaban Mugabe aka yi haka.

5- Sani Abacha

Jana Sani Abacha ya zama shugaban kasa a shekarar 1993 bayan ya hambarar da gwamnatin Shonekan, zuwa shekarar 1998 da ya rasu, Mugabe ya san da shi.

6- Abdulsalam Abubakar

Janar Abdulsalam Abubakar ya kama madafan iko ne bayan rasuwar Abacha, inda yayi mulki daga shekarar 1998, zuwa 29 ga watan Mayun 1999.

Abdulsalam Abubakar ne yayi mulkin Soja na karshe a Najeriya, inda ya mika mulki zuwa Cif Olusegun Obasanjo a 1998 a karkashin mulkin fara hula, mulkin Dimukradiyya, inda shima a shekarar 2007 ya mika ma marigayi Umaru Musa Yar’adua, wanda ya rasu a shekarar 2010.

Jerin shuwagabannin Najeriya da suka yi zamani da Mugabe tsawon shekaru 37 da yayi a karagar Mulki
Mugabe da Yar'adua

Bayan rasuwar Yar’adua, sai mataimakinsa, Goodluck Jonatha ya dare kujerar shugaban kasa a shekarar 2010, inda shima ya mika ragamar mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu a shekarar 2015.

A jimlacea iya cewa Najeriya ta canza shuwagabanni sai 10 a zamanin mulkin Mugabe, amma tayi shuwagabannin kasa guda 9, idan aka lissafa Buhari yayi zuwa biyu a tsakankanin mulkin Mugabe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng