Jerin Attajiran matasan Arewa su 20 da suka yi zarra a sha’anin Kasuwanci

Jerin Attajiran matasan Arewa su 20 da suka yi zarra a sha’anin Kasuwanci

Bincike ya bankado wasu jajirtattun matasan Arewa su 20 da suka yi zarra a sha’annin kasuwanci, suka tara arziki, kuma duk basu haura shekaru 40 ba!

Gidan Talabijin na Nishadi ne ya gudanar da wannan bincike, inda ya bayyana matasan a matsayin mutane masu kishin yankin Arewa, kuma sun taimaka sosai wajen rage zaman banza ga sauran matasa ta hanyar basu ayyukan yi.

Ga dai jerin yan kasuwan nan:

Haowa Bello: sunan kamfanin Madam Coquette, kuma ta shahara wajen dika jakukkuna masu tsada a Najeriya, a yanzu haka tana da rassa a Amurka, da wasu kasashen Turai, har ma kasashen Afirka.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi arba da jami’an FRSC, sun kashe 1 sun tafi da 2

Usman Dantata Karami: Sunan kamfaninsa ‘Anadariya Farms’, kuma tsohon maikacin banki ne, inda a yanzu ya cirri tuta wajen noma, inda yake nomawa, gyarawa tare da sarrafa amfanin noma.

Hadiza A Muhammad: Sunan kamfanin ta ‘Bilyak Consulting Limited’, ita ma tayi aiki da babban bankin Najeriya, sa’annan tayi aiki da kamfanin Microsoft dake Najeriya. Ta shahara wajen tallafa ma matasa masu bukatar jari ko koyon sana’an hannu.

Zarah Indimi: itace shugaban shahararren wajen cin abinci mai sunaTulipBistro & Rice Bowl dake garin Abuja, sun kware wajen dafa abinci irin na gida, har ma dana kasashen waje daban daban, a yanzu haka ta fadada kasuwanci zuwa garuruwa da dama, a haka tana samar ma jama’a aikin yi.

Rilwan Hassan: sunan kamfaninsa ‘Focal Point Cleaners’, wanda suka yi suna wajen iya wanke kayan sawa da ire irensu ta hanyar amfani da na’urorin zamani. Shine ya assasa gidauniyar Sardauna Child Foundation, wanda take daukan nauyin marayu. A yanzu kamfaninsa ya fadada zuwa ayyukan gine gine, noma da buga takardu.

Jerin Attajiran matasan Arewa su 20 da suka yi zarra a sha’anin Kasuwanci
Jerin Attajiran matasan Arewa su 20

Abdulrahman Aliyu: Shugaban kamfanin Zavati Group, hamshakin kamfani a fagen gine gine, juya kudi, da kuma zuba hannayen jari, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Laura Ahman: sunan kamfaninta ‘Laura Ahman Brand’, ta kware wajen hada takalma zafafa da siyar dasu, kuma ana samun takalman nata a duk fadin kasar nan.

Nasir Yammama: shugaban kamfanin ‘Verdent Agri-Tech’, kuma yana da kwarewa a fannin kere kere, amma yafi karfi a sha’anin noma, inda yake amfani da iliminisa wajen wayar ma manoma kai tare da basu iri mai inganci.

Laylah Ali Othman: Ita kuma ta tsaya ne a bangaren kayan kwalliya na ciki daki, don haka ta kafa kamfanin L and N Interiors’, sa’annan tana sana’ar buga mujallun zamani, tare da cewa ita kanta yar kare hakkin mata ce.

Huda Fadoul Abacha: sunan kamfanin Hudayya, wanda suka kware wajen dinkin, musamman cinikin kayan amare.

Fantis Mohammed: Ta fito ne daga jihar Borno, inda ta kafa kamfanin ‘H Magnet’ wanda suka hada kayan sawa, sa’annan ta kafa ‘Nowrie’ dake aikin dinka kaya.

Labila Kabir: ita ce shugaban kamfanin ‘Asoebicouture’, da yayi suna wajen ita dinka kayana sawa, na kyalekyale tare da iya sarrafa yadi.

Hyaledzira Laushi: Laushi ta shahara ne a wajen iya shirya wuraren biki, wanda hakan ya kai tag a kafa kamfanin ‘Blueeyelvetmarquee’.

Khalifa Dankadai: shine shugaban kamfanin Khalifa Dankadai & Company, shi kuma yayi suna wajen taimaka ma kananan yara almajirai, tare da ilimantar dasu, da koya musu sana’a.

Fatima Mamza: kowa da sana’ar data karbe shi, kamfaninta Mamza Beauty Limited ya shahara wajen shirya ma mata kwalliya da kuma gyaran jiki, musamman ga Amare.

Samira Garba Abari: Sunan kamfaninta Patooty Nigeria Enterprise, suna hada man shafawa, irin su man kwakwa, man kadai a zamanance.

Muhammad Ibrahim Jega: Muhammad ya shahara wajen kirkire-kirkire, kuma dan gwagwarmaya ne, shine shugaban kamfanin ‘Start up Arewa’

Mukhtar Ibrahim Aliyu: sunan kamfaninsa Urban Abode, kuma suna harkar gine gin gidaje, kasuwanni da ofishoshi, haka zalika kwararren mai zane zanen gidaje ne.

Mairo Abdullahi: Ita kuma wannan jajirtacciyar matashiyar ta yi suna ne wajen shirya bikin Kamu, na al’adar hausa, ta hanyar zamanantar da shi, sunan kamfanin ‘Kamu Décor’.

Fatima oyizah Ademoh: Yar asalin jihar Kogi, Malama ce a jami’a, kuma yar kasuwa ce ita, ta samar da wuta a kauyuka a karkashin shirin ta mai suna Ajima farmsa off-grid Energy.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel