Yadda Mohammed Salah yake jawo ra’ayin Turawa zuwa Musulunci da harkar ƙwallo
Da dama daga cikin magoya bayan kungiyar Liverpool sun nuna jin dadinsu da namijin kokarin da dan kwallon kasar Misra, wanda ke taka leda a kungiyar kwallon, Mohammed Salah ke yi.
Magoya bayan kungiyar, wanda yawancinsu Turawa ne sun nuna sha’awar addinin Musulunci saboda Mohammed Salah, inda wasu daga cikinsu ma suke ganin tamkar da’awah yake yi a cikin Fili.
KU KARANTA: Tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari yayi jimamin mutuwar tsohon mataimakinsa
Bayan kammala wasan Liverpool da Southampton a ranar Asabar, inda Mohammed ya ci kwallaye biyu, inda aka tasbi 3-0, wani dan wasun Liverpool ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa “Tunda Salah ya kara ci, toh na Musulunta.”
Tun daga nan an ci gaba da samun magoya baya da dama dake nuna sha’awar shiga addinin Musulunci saboda Mohammed Salah. zuwa yanzu dai Salah yaci kwallaye 14 a wasanni 18.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng