An cigaba da cinikin baƙaƙen fata a matsyain bayi a kasar Libya, larabawa na gwanjon su
Wani labari da gidan jaridar CNN ta fasa a satin daya gabata na nuni da cewa a yanzu haka ana cinikin bakaken fata a kasar Libya, inda ake siyar dasu a matsayin bayi.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito da dama daga cikin dubunnan bakin hauren dake shiga kasar Libya daga kasashen yammacin Afirka ciki har da Najeriya da nufin tsallakawa nahiyar Turai na shiga tasku a Libya.
KU KARANTA: Dangote yayi ɓarin kuɗi a bikin ƙaddamar da littafin marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi I
Da fari dai ana fara tara su ne a sansanin bakin haure a Libyan, zuwa lokacin da sansanin ya cika, suka rasu wajen zuwa, ko kuma idan basu da kudin biya a tsallaka dasu zuwa nahiyar Turai, sai a fara siyar dasu.
Cikin wani bidiyo da CNN ta dauko yayin da ake kada ma bayin kararrawa, an jiyo Larabawan suna bayyana bakaken fatan a matsayin ‘Haja’, sai dai gwamnatin kasar Libya ta nuna damuwarta dangane da lamarin, kuma ta sha alwashin bincikar lamarin.
Mataimakin shugaban kasar Libya, Ahmed Metig ya bayyana cewa zai kafa kwamitin bincike, don tabbatar da an kama dukkanin masu hannu cikin bahallatsar.
Yayin da ake siyar da wasu bakaken fata a matsayin bayi, wasu matan yan Najeriya kuma jefa su ake yi cikin harkar karuwanci da karfi da yaji, inda alkalumma suka bayyana cewa kashi 80 na yan Najeriya mata karuwanci suke yi a kasar Italiya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng