Gasar zakarun Turai: Kungiyar Real Madrid zata kara ba tare da fitattun 'yan wasan ta 4 ba
Labaran da ke iso mana dai suna nuni da cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata buga wasan ta na yau tsakanin abokan hamayyar su a yau ba bu fitattun 'yan wasan su akalla hudu a cigaba da gudanar da gasar cin kofin zakarun turai.
Fitattun 'yan wasan da kungiyar tayi rashin su sun hada da jagoran kungiyar kuma shugaban ta Sergio Ramos, sai kuma Keylor Navas, Gareth Bale da Mateo Kovacic.
KU KARANTA: Wasu malaman makaranta sun kara faduwa jarabawa
Legit.ng dai ta samu cewa jagoran tawagar, Ramos ya kare hanci ne a yayin wata arangama da ya samu da dan wasan baya mai tsaron gida na kungiyar Atletico Madrid a wasan da suka kara a karshen sati da suka tashi kunnen doki babu wanda yaci wani.
Kafin nan dai mai horas da kungiyar ta Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana fatar sa ta samun wasu daga cikin yan wasan kafin wasan na yau to amma dai kungiyar tuni har ta shilla zuwa kasar ta Cyprus inda zau kara ba tare da yan wasan ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng