Sabon Labari da dumi-duminsa: Ta Mugabe ta kare!

Sabon Labari da dumi-duminsa: Ta Mugabe ta kare!

- Robert Mugabe ya shafe kusan shekaru 40 yana mulkar Rodhesia, wadda ya canzawa suna zuwa Zimbabwe

- Sojoji sun yi masa kawanya a gidansa tun a makon jiya, sun masa darin talala na cikin gida

- Sun tilasta masa murabus amma ashe ki yayi

Robert Mugabe na ji yana gani mulki ya karasa subuce masa daga hannunsa, kuma a hotunansa na makonan nan fuskarta ta nuna shi cike da damuwa, tsufansa ya sake fitowa fili,

Sabon Labari da dumi-duminsa: Ta Mugabe ta kare!
Sabon Labari da dumi-duminsa: Ta Mugabe ta kare!

Daga karshe dai, a yau Lahadi, ta shugaba Robert Mugabe, mai kishin kasar Zimbabwe, mai kokarin kwatowa bakaken fata hakkinsu (daga turawa) na kasar Rhodesia wadda ya canza wa suna zuwa Zimbabwe ta zo karshe.

Babbar Jam'iyyar su ta ZANU-PF ta sauke shi daga shugabancin kasar sa, bayan da ya ki yayi murabus duk da shekarunsa 94 da haihuwa, kuma bashi da cikakkiyar lafiya.

DUBA WANNAN: Matsalar shaye-shaye ta zama sai Inna lillahi

An kula cewa matarsa, Grace, mai shekaru 50da haihuwa yake so ya dora a matdsayin mai jiran gadon mulki, bayan da ya sauke mataimakansa a karo na wajen 3 a shekarun nan.

Takunkumai da turawa dai suka kakabawa kasar ta Zimbabwe bayan da Mugabe ya kwace gonakin turawa ya mayarwa da bakaken fata sun ruguza tattalin arziki na kasar, inda albashi sai a gingimari ake karbar sa, sayen burodi kuwa, wheel barrow ake turawa cike da kudi marasa daraja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Saukarsa daga jam'iyyar na nufin mulki ya subuce daga hannunsa kenan. Kuma mataimaki na karshe da ya sauke ne makonni biyu da suka wuce suka dora a matsayin shugaba, wanda ga dukkan alamu shi zai zama sabon shugaba.

Jam'iyyar ta kuma sauke da ma korar matarsa Grace Mugabe daga mukamai na jam'iyyar, an kuma gano jerin motoci na barin fadar shugaban kasa a yau dinnan, jama'ar gari kuwa suna ta rawa da sowa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng