Lema ta yage: Tsohon Gwamnan Ebonyi ya jagoranci mutane 6,000 zuwa APC
Shugaban jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC mai suna Cif John Odigie-Oyegun ya karbi tsohon gwamnan jihar Ebonyi da matar sa Josephine Elechi zuwa jam'iyyar ta su daga jam'iyyar PDP.
Haka ma dai mun samu cewa akalla wasu mutane 6,000 da suka sauya shekar zuwa jam'iyyar ta APC cikin su kuwa hadda tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ta PDP a yankin kudu maso gabas mai shuna Cif Solomon Onwe.
KU KARANTA: Malami a jami'ar jihar Kwara ya kashe kansa
Legit.ng dai ta samu cewa yayin da shugaban jam'iyyar ta APC yake karbar tasu, ya bayyana cewa tabbas sun yi zabe mai kyau don kuwa jam'iyyar tana da dukkan abun da suke bukata sannan kuma zata basu cikakkiyar dama dai-dai da dukkan 'ya'yan ta.
Haka ma dai Cif Oyegun ya kara da cewa yanzu haka jam'iyyar ta APC tana da gwamnoni 24 cikin 36 dake a kasar sannan kuma ya kara da cewa za su lashe zaben da yanzu haka ake gudanarwa a jihar Anambra.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng