Kalli jerin sunayen sabbin kwamishinonin jihar Neja, su 18
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello ya aika ma majalisar dokokin jihar sunayen mutane 18 dayake muradin nadawa kwamishinoni domin tantancewa.
Cikin wata wasika da gwamnan ya aika ma majalisar a ranar Alhamis, kuma Kaakakin majalisar, Alhaji Ahmed Marafa ya karanta, yace yayi hakan ne bisa bin sashi na 192 (2) na kwaskwarararren kundin tsarin mulki, shekarar 1999.
KU KARANTA: Shugaba Buhari da Osinbajo za su kashe Naira Biliyan 2.5 a kan Motoci da tafiye-tafiye
Sunayen daya aika sun hada da Idris Amin daga karamar hukumar Katcha, Zakari Bawa daga Lapai, Zakari Abubakar daga Bidda, Ibrahim Panti daga Lavun, Umar Tagagi daga Agaei, Hajiya Ramatu Yardua dag Edati , Dr Jibrin Mustapha daga Chanchanga, Mamman Musa daga Bosso, Amina Gu’ar daga Paikoro da Ismail Ibrahim daga karamar hukumar Shiroro.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito sauran sun hada da Ibrahim Balarabe daga karamar hukumar Rafi, Danjuma Sallau daga Munyan, Fatima Madugu daga Mashegu, Zakari Jikantoro daga Agwara, Nasara Dan Malam daga Magama, Isah Kanko daga Wushishi, Kabiru Musa daga Mariga sai kuma George Koce daga Gurara.
Bayan karanta wasikar, sai majalisar ta amince da fara tantancewa sunaye daga watan janairun shekarar 2018.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng