Najeriya ta samu rangwamen N7bn a fitowa gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

Najeriya ta samu rangwamen N7bn a fitowa gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

- Za'a yi gasar a Rasha a 2018

- Najeriya ta fito tun kan a gama kwalifayin

- Ta sami ragin kudin saboda an ki tura 'yan agajin task fos

Gwamnatin Najeriya ta baiyana cewa ta samu ragin kashe kudi har N7bn a kan kungiyar kwallon kafa ta Sufa Iguls a yayin da suke gumurzun fitowa gasar zakarun cin kofin kwallon kafa ta duniya saboda ba'a hada 'yan kwallon ba da kungiyar agaji ta task fos.

Ministan motsa jiki, Solomon Dalung, ne ya baiyana haka a Abuja a ranar Talata.

Kungiyar Sufa Iguls
Kungiyar Sufa Iguls suna murnar fitowa gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

"Wannan ragin kashe kudin da aka samu ya samo asali ne daga hadin gwiwar NFF da Sufa Iguls da suka ki yarda a hada su da 'yan agajin."

Najeriya ta fito gasar zakarun cin kofin kallon kafa na duniya wacce FIFA take shiryawa tun ana saura wasa daya a kammala gasar kwalifayin na nahiya-nahiya.

Za'a yi wasan a shekara 2018 a Rasha.

DUBA WANNAN: Ziyarar shugaba Buhari yankin kudu maso gabas za ta kawo hadin Kai - Gwamna Rochas

Ministan ya ce kowa na iya bincikawa ya gani. Saboda kin hada su da 'yan agajin task fos an rage kashe kudi sosai.

Ya gama da cewa fitowa Sufa Iguls gasar ya samo asali ne daga kwarin gwiwa da kuma goyon bayan kowanne dan Najeriya ya bayar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng