Kotu ta daure wani dattijo bisa amfani da kudin bogi

Kotu ta daure wani dattijo bisa amfani da kudin bogi

- Kotu ta daure dattijo mai anfani da kudin bogi

- An bashi daurin shekara 1 gidan yari

- Hukumar EFCC zata halaka kudin

Dattijo mai suna Hussaini Baba wanda Hukumar EFCC da ke yankin Kaduna take tuhuma game da kama shi da ka yi da kudin bogi, an kama shi da mallakin Naira 180,500 kwayar Naira dari biyar-biyar.

A ranar Laraba 15 ga watan Nuwamnba, 2017 babbar Kotu da ke jihar Kaduna ta bawa dattijon daurin shekara 1 gidan yari ba tare da cin shi tara ba.

Kotu ta daure wani bisa buga kudi na bogi
Kudaden bogi mallakin Hussaini Baba

A san da aka tsai da shi gaban shari’a a watan Oktoba, 2017 Hussaini Baba ya musa zargin da ake masa bayan nan ne aka daga karar zuwa ranar Laraba 15 ga Nuwamba, 2017 don cigaba da binciken sa.

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi yayi kira da a yi wa matar da aka yi wa kisan gilla a Kano adalci

Kotu kuma ta ba hukumar Yaki da cin hanci da ta gaggauta hala kudadden.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng