Hukumar ICPC ta kama tsohon mai shari’ar jihar Kano
- Hukumar ICPC ta cafke tsohon mai shari’a na jihar Kano akan zargin cin hanci da rashawa
- Ana zargin mai shari’a Auta da kula makirci da aikata ba daidai ba
- Mai shari’a Auta tare da wasu mutane sun zalunci wani dan kauwar Kano naira miliyan 220
Hukumar yaki da cin hanci da sauran laifuffukan, ICPC, ta bayyana cewa ta kama tsohon mai shari’a na ihar Kano kan zargin cin hanci da rashawa da aikata laifuka.
A wata sanarwar da kakakin hukumar, Rasheed Okoduwa ya fitar, ya ce hukumar ta cafke mai shari’a Kabiru Mamman Auta a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamban shekarar 2017.
Okoduwa ya ce an kama shi ne a lokacin da ya ziyarci ofishin hukumar don amsa tambayoyi akan zargin da aka masa cewa ya kulla makirci tare da wasu mutane don zaluntar wani dan kasuwa a Kano, Alhaji Bashir Sani Kwangila Yakasai (SKY), na naira miliyan 220.
Ya ce an gabatar da batun a gaban hukumar ne bayan da aka kai kara a hukumar shari'a na kasa wadda ta kafa kwamiti don bincika zargin.
KU KARANTA: Sarki Sanusi yayi kira da a yi wa matar da aka yi wa kisan gilla a Kano adalci
Okoduwa ya ce wadanda ake zargin, mai shari’a Auta da Bashir Sufi sun karbi wannan kudi daga hannun Alhaji Yakasai ta hanyar da bai dace ba, cewa sun yi hakan ne a madadin babban tsohon mai shari’a na kasa, Aloma Mukhtar.
Ya kara da cewa, Mai shari’a Auta a cikin jawabinsa ga hukumar ICPC ya bayyana cewa ya mayar wa Yakasai naira miliyan 20 daga cikin kudin.
"An bada belin mai shari'a Auta daga tsare, yayin da bincike kan batun zai ci gaba", in ji ICPC.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng