Mata ta nemi a raba auren ta da mijin ta saboda rashin kuzari wajen Jima’i
- Kate Ude ta roki alkali ya raba aurenta da Micheal Ude sabo da rashin gamsar da ita a akan gado
- Kate ta ce minti daya Micheal ya ke yi akan gado
- Micheal Ude ya ce Kate ta yawan zuwa masa na a lokacin da bai da sha'awa kuma shi baya shan maganin karfi maza
Wata mata mai shekaru 32, Kate Ude ta roki alkalin babbar kotun birnin tarayya Abuja dake Jabi da ya raba auren su da mijinta, Michael Ude, saboda rashin gamsar da ita wajen jima’i.
Matar ta fadawa kotu cewa mijinta ba namiji bane. “Na yi haukuri da shi amma ya kai ni makura duk lokacin da muka zo kwanciya sai ya kasa yin komai, sai kamai-kamai a cikin minti daya sai kaga ya gama”.
Kate Ude ta fadawa kotu cewa warware aurenta da Micheal Ude shine ya da ce da ita.
KU KARANTA : Ka kaddamar da makiyayan Fulani a matsayin yan ta’adda – Hon Gyang ya roki Buhari
Da Micheal Ude ya kai nasa bayyanain a kotu, y ace mafi akasarin lokacin da take zuwa masa baya cikin sha’awa shine yasa sai abin ya gagara kuma shi baya shan wani magani domin samun karfin saduwa da matar sa.
Shima ya amince da araba auren.
Alkalin Kotun, ya daga ci gaba da sauraronkaran sai watan Fabrairu na shekara 2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng