Karayar arziki: Dangote ya sayar da kamfanin taliyar sa akan Naira biliyan 3.75

Karayar arziki: Dangote ya sayar da kamfanin taliyar sa akan Naira biliyan 3.75

Wani sashe na babban kamfanin nan mallakar hamshakin mai kudin nan dan asalin jihar Kano, Alhaji Aliko Dangote daya shahara wajen samar da filawa da taliya ya sayar ya bangaren samar da taliyar yara kan makudan kudaden da suka kai darajar Naira biliyan 3.75.

Dangote din dai kamar yadda muka samu ya sayar wa da wani kamfanin da ya kware wajen samar da taliyar yara din mai suna De United na kasar waje kamfunnan nasa har guda biyu dake a garin Ikorodu da kuma garin Calabar dake a jihohin Legas da kuma Kuros Ribas.

Karayar arziki: Dangote ya sayar da kamfanin taliyar sa akan Naira biliyan 3.75
Karayar arziki: Dangote ya sayar da kamfanin taliyar sa akan Naira biliyan 3.75

KU KARANTA: Wani dan sanda yaje sata ya baro katin shaidar sa

Legit.ng haka zalika ta samu dai cewa wannan ma dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da mashahurin dan kasuwar ya sayar da hannun jarin sa da yakai darajar Naira biliyan 27 ga wasu fitattun yan kasuwa daga kasashen waje.

To sai dai, a nasu bangaren, mahukuntan dake kula da kamfanonin sun bayyana cewa sun sayar da bangaren samar da taliyar yara din ne domin su samu damar tattara hankulan su wajen samar da filawa da taliyar manya ne kawai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng