Najeriya ta lallasa Ajantina ci 4-2, Sergio Aguero ya suma

Najeriya ta lallasa Ajantina ci 4-2, Sergio Aguero ya suma

Yan kwallon Super Eagles sun rama biki a kan kasar Ajantina a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, inda suka ragargaji Ajantina, tare da yi musu ruwan kwallaye a ragarsu a filin wasa dake Krasnodar, a kasar Rasha.

BBC ta ruwaito yan wasan Najeriya da suka hada da Kelechi Iheanacho, Alex Iwobi da Brian Idowu ne suka zura kwallaye a ragar Ajantina, bayan Aguero da Banega sun fara zura ma Najeriya kwallaye biyu.

KU KARANTA: Nagari Nakowa: Kalli kyawawan hotunan Buhari sanye da kayan kabilar Ibo

A minti na 17 ne Sergio Aguero, dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ya bude wasan da kwallo guda a zaren Najeriya, inda a minti na 34, Eva Banega ya kara ma kasar Ajantina.

Najeriya ta lallasa Ajantina ci 4-2, Sergio Aguero ya suma
Super Eagles

Har sai da aka kai minti na 45 ne, sannan Super Eagle ta fara rama biki, ta hannun Iheanacho, wanda ya zura kwallon farko ma Najeriya daga bugun taki, bayan nan sai Alex Iwobi dan Arsenal ya kara kwallo daya, daga nansai Iwobi ya kara, sai kuma Brian Idowu ya rufe wasan da nasa kwallon.

Sai dai kafin a dawo hutun rabin lokaci, majiyar Legit.ng ta ruwaito dan wasan gaba na Ajantina, Aguero ya fadi sumamme yayin da ake hutun a cikin dakin canja kaya, inda nan da nan aka garzaya da shi zuwa Asibiti.

Najeriya ta lallasa Ajantina ci 4-2, Sergio Aguero ya suma
Aguero

Bayan kammala wasan ne hukumar kwallon kafa ta Ajantina ta tabbatar da suman Aguero, inda tace bincike ya nuna bashi da lafiya tun kafin wasan, amma kungiyar Man City tace tuni aka ba Aguero daman komawa Ingila.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng